Labarai

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta mayar da Samuel Anyanwu kan kujerarsa ta Sakataren jam’iyyar na ƙasa.

Mai riƙon muƙamin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Iliya Damagum ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba.

Yayin taron dai, shugaban na tare da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Damagum ya ce yanke shawarar dawo da Anyanwu cikin kwamitin zartarwar jam’iyyar na ƙasa shawara ce mai wahalar gaske, amma ta sami goyon bayan mambobin kwamitin da dama.
Ya kuma sanar da cewa PDP ta soke taron kwamitinta na zartarwa da a baya aka yi yunkurin yi amma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba da shawarar dakatarwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button