Ketare

Bisa ga dukkan alamu yarjejeniyar tsagaita wuta da ba ta da tabbas da aka ƙulla tsakanin Isra’ila da Iran, bayan fushin da Shugaba Trump ya nuna a kan batun ta fara aiki.

Shugaban Amurkan ya zargi ɓangarorin biyu da saɓa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka ƙulla tun da farko.

Bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Mista Trump da Benjamin Netanyahu, ofishin firaministan Isra’ilan ya fitar da sanarwar da ke cewa sun dakatar da hare-harensu.

Shi ma shugaban Iran ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar, idan har Isra’ila ba ta canza matsaya ba.

Kawo yanzu dai ƙasashen biyu sun fara sanar da sassauci a kan matakan da suka tsaurara a baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button