Labarai
Majalisar Dokoki ta kasa ta ce ta aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kudurorin dokar harajin da ta amince da su a hukumance domin ya sanya musu hannu su zama doka.

Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja.
A bara ne dai Tinubu ya aike wa majalisar kudurorin domin su yi nazarinsu sannan su amince da su a matsayin doka.
Kudurorin dai a baya sun yamutsa hazo sosai a zaurukan majalisun da ma a fadin kasa, kafin daga bisani majalisun na wakilai da dattawa su amince da su.



