Daga yau Laraba 18 ga watan Yunin 2025 kamfanonin sadarwa a kasarnan zasu dinga cire kudin saƙwannin da bankuna suke turowa na kai-tsaye daga kudin katin da kwastomominsu suka saka.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar kamfanonin sadarwa masu lasisi na Najeriya (ALTON) Gbenga Adebayo,, da sakataren yada labaran ta Damian Udeh.
A cewar Adebayo, wannan sauyin ya zo daidai da matakin da Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta yi na daidata farashin sakwannin da bankuna suke turowa kwastomominsu, wanda aka yi tare da hadin guiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) da sauran masu ruwa da tsaki.
Shugaban na ALTON ya ce sabon tsarin biyan kudi zai baiwa masu amfani da hanyar sadarwar wayar damar cajin abokan ciniki kai tsaye idan suka yi amfani da manhajar bankunansu , tare da cire kudaden daga kudin wayarsu akan Naira 6.98 akan kowanni sakan 120.
Ya lura cewa abokan ciniki za su sami sakon neman izinin acire kudin kafin a dauki kudin ,kuma za’a cire kudin ne kawai idan anyi nasarar cirar kudi ko kuma wani abun akan manhajar.




