Labarai
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sanya hannu kan sabbin dokokin sauya tsarin haraji na ƙasar a yau Alhamis.

Wannan matakin dai ana sa ran zai sauya tsarin tattara haraji da kuma inganta yanayin kasuwanci a Najeriya.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labaru, Bayo Onanuga ta ce sabbin dokokin huɗu sun haɗa da dokar haraji ta ƙasa da dokar tafiyar da lamuran haraji da dokar kafa hukumar haraji ta Najeriya da kuma dokar kafa ma’aikatar kula da hukumomin tattara haraji ta Najeriya.
Majalisar Dokoki ta kasa ce za ta amince da su bayan shawarwari da dama daga masu ruwa da tsaki.



