Tsohon Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya tsallake rijiya da baya

A ranar Juma’a bayan da motocinsa suka ci karo da harin bindiga mai tsanani daga ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno
An ce ‘yan ta’addan ne suka kitsa harin, lamarin da ya kara jefa al’umma cikin damuwa dangane da tabarbarewar tsaro a yankin.
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television da yammacin Lahadi.
A cewar Ndume, an kai wa Buratai da dakarun da ke tare da shi hari ne a kusa da wata sansanin sojoji da ke kan gaba da fagen fama.
Ko da yake ba a bayyana cikakkun bayanai game da asarar da aka yi ba, Ndume ya ce an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ‘yan ta’addan da dakarun da ke rakiya Buratai.
Dakarunsa sun mayar da martani cikin jaruntaka, amma ‘yan ta’addan sun lalata kayayyakin yaki da dama.”




