Jakadun G7 sun nuna goyon baya ga Ukraine, tare da gargadin Rasha da karin takunkumi

Ministocin harkokin wajen kasashen G7 sun hadu a matsayin nuna hadin kai, inda suka cimma yarjejeniya kan wata sanarwa ta hadin gwiwa da ke tabbatar da goyon baya ga cikakken ikon Ukraine kan yankinta yayin da suke gargadin Rasha da ta bi jagorancin Kyiv wajen karbar tsagaita wuta – ko kuma ta fuskanci karin takunkumi.
Taron, wanda aka gudanar a garin La Malbaie a Quebec, ya gudana tsawon kwanaki biyu a cikin yanayin na tashin hankali na diflomasiyya, musamman game da manufofin Amurka kan kasuwanci, tsaro, da Ukraine.
Duk da kalubalen da suka fuskanta, ministocin G7 sun sami damar gabatar da taron hadin kai a ranar Jumma’a, suna masu kawar da fargabar cewa Rasha ko China za su iya amfani da rarrabuwar kawuna.
Kungiyar kasashen masu karfin tattalin arziki a Duniya G7 – wadda ta ƙunshi Biritaniya, Canada, Faransa, Jamus, Italiya, Japan, da Amurka tare da Tarayyar Turai – ta nuna haɗin kan ta a cikin sanarwar ƙarshe, ta sake tabbatar da “goyon bayanta marar yankewa ga Ukraine wajen kare cikakken yankinta, ikon mulki, da ‘yancin kai”




