Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gamsu da ƙoƙarin ƙungiyar ci gaban kasuwar singer bisa kwashe magudanan ruwa domin kauce wa ambaliya a yankin.

Kwamishinan harkokin karkara da ci gaban al’umma, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, wanda daraktan ci gaban jama’a na na’aikatar, Alhaji Bashir Tijjani, ya wakilta ne ya bayyana hakan yayin duba yadda ake gudanar da aikin gyaran magudanan ruwa daga titin Bello zuwa titin Abdullahi Bayero a karamar hukumar Fagge.
Ya bayyana cewa ya zama dole a jinjinawa matakin da suka ɗauka sakamakon ƙoƙarin da gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi na hana ambaliya, musamman a lokacin da damina ke cigaba da kankama.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin aikin gayya na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Garba Kofar Naisa, ya buƙaci gwamnatin jihar da ta sake gina titin Bello domin hana ambaliya, tare da kira ga sauran ƙungiyoyin kasuwanni su yi koyi da Kasuwar Singer wajen tsaftace muhalli domin kau cewa abinda zai haifar da asarar dukiya da rayukan


