Ketare
A ina cibiyoyin nukiliyar Iran suke kuma waɗanne ne aka kai wa hari?
Hotunan tauraron ɗana'dam da suke nuna cibiyar Natanz da aka ɗauka a watan Janairun 2025

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hare-hare a cibiyoyin nukiliya na Iran a ranar Juma’a 13 ga watan Yuni. Wasu faye-fayen bidiyo da BBC ta gani sun nuna yadda hare-haren suka wakana a cibiyoyi guda biyar.
Yawancin cibiyoyin a babban birnin ƙasar, Tehran suke – inda wasu faya-fayen suka nuna yadda hare-haren suka ɓarnata wasu gidajen mutane.
Wata babbar cibiya ita ce Natanz – kimanin kilomita 225 (mil 140) daga kudancin babban birnin ƙasar – inda cibiyar haɓaka ma’adinin uraniun yake.
Rahotanni daga Iran sun nuna cewa cibiyoyin Natanz da Arak suna cikin cibiyoyin da Isra’ila ke hari.
Amma ita kuma Iran ta nanata cewa ba domin samar da makaman soji take shirin nukiliyarta ba.




