Labarai
Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Tinubu, ta bukaci al’umma musamman mata da su baiwa maza tallafi da yanayin da zai basu damar gudanar da aiki yadda ya kamata a matsayinsu na iyaye maza.

Remi na wannan jawabin ne a yau, a babban birnin tarayya Abuja, a wani bangare na bikin Iyaye maza ta duniya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ranar Uba ta duniya, rana ce da aka kebe domin girmama iyaye, da kuma matsayin uba, da tasirin sa a cikin al’umma.
Ta kara da cewa tana jinjina wa duk wani uba a fadin kasar nan da suka sadaukar da kansu wajen baiwa yayan su tarbiyya.




