Iran ta kaddamar da harin makami yayin da Isra’ila ta kai hari kan Tehran karo na uku a rana

Mutanen Iran da Isra’ila sun wayi gari cikin hayaki da rusassun gine-gine a ranar Lahadi bayan abokan gaba sun fadada hare-harensu a daren, inda Isra’ila ta kai hari kan ma’aikatar tsaron Tehran, kuma Iran ta saki ruwan makamai masu linzami masu kisa.
An ji karar siren na harin sama da fashe-fashe daga acewar ‘yan jaridar kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP a biranen Urushalima da Tel Aviv da safiyar Lahadi, yayin da sojojin Isra’ila suka ce miliyoyin Isra’ilawa suna “gudu don samun mafaka” a fadin kasar.
Hukumar agajin gaggawa ta Isra’ila ta ce aƙalla mutane takwas, ciki har da yara, sun mutu a hare-haren da aka kai da daddare, kuma kusan 200 sun jikkata.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya lashi takobin kai hari kan “kowace manufa ta gwamnatin Ayatollah”, yayin da shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin kara kai hare-hare za su haifar da nuna “matsayi mai tsananin karfi”.




