Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na inganta ilimin addinin islama ta hanyar horas da malamai da kuma kara baiwa kwararru horaswa ta musamman
KANO ISLAM

Kwamishinan Ilimi na Jihar Dr. Ali Haruna ne ya ba da tabbacin hakan a jiya asabar, yayin da yake bbude taron karawa juna sani na kwanaki 2 da aka shirya wa malaman makarantun Sakandare na Alkur’ani da kuma harshen Larabci.
Dr.Makoda ya bayyana cewa, a yayin da gwamnati ke ba da fifiko wajen samar da ingantaccen ilimi, za ta ci gaba da bullo da aiwatar da wasu tsare-tsare da zasu taima wajen inganta ilimin addinin Musulunci.
Kwamishinan wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha Farfesa Dahiru Muhammad Saleh ya ce an shirya taron horaswar na kwanaki 2 domin baiwa malaman makarantun Sakandare na Larabci sabbin dabarun koyarwa na zamani.




