Labarai
Ƙungiyar Malaman makaranta ta NUT ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya dawo da martabar malamai da walwalarsu a Nigeria domin janyo hankalin matasa su rungumi aikin koyarwa yadda yakamata

Shugaban kungiyar ma ƙasa Kwamared Audu Amba ne ya yi wannan kira a wata hira da ya yi da manema labaru Abuja.
Audu ya buƙaci gwamnati da ta ɗauki malamai a matsayin abin koyi tare da fahimtar cewa aikin koyarwa ginshiƙi ne na ginin al’umma.
Audu Amba ya sake bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda aka mayar da aikin malunta a Nigeria wanda ya ke a matsayin zaɓi na tilas a tsakanin masu neman aiki .
Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta fitar da manufofi na musamman domin ɗaga darajar malamai fiye da sauran ƙwararru tare da sanya aikin koyarwa a matsayin zaɓi na farko da matasa za su dinga nema.
Amba ya bukaci gwamnati da ta koyi darasi daga ƙasashen da ke girmama malamai kamar kasar Finland, inda aikin koyarwa ke da daraja da girmamawa.




