Yadda waya da adashi ke haifar da mace-macen aure a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, ƙungiyar harkokin addinin Musulunci ta ƙasar (AIN), ta danganta yawan mace-macen aure da ƙasar ke fama da shi da wasu manyan abubuwa guda uku da suka haɗa da auren mace fiye da ɗaya, da wayar salula da kuma adashi.
Ƙungiyar wadda ke da alhakin sasanta rigingimun ma’aurata ta ce a shekarar da ta wuce ta 2024, ta raba aure 1,433 a birnin Yamai.
Haka kuma a rahoton da ta fitar ƙungiyar ta ce ta yi nasarar sulhunta aure 2,565.
Rawar da wayar salula ke takawa: Isa Karimu wani ɗan jamhuriyar Nijar ya ce ya kamata malamai su ƙara ƙoƙari su yi wa’azi wajen nusar da jama’a cewa aure ibada ne sannan a lura da irin rikicin da wayar salula ke haɗawa.
” Ni kaina idan na shiga gidana to zan ajiye waya ne sai kuma idan zan fita. Saboda da zarar waya ta yi ƙilin to dole ne hankalin maiɗakinka ya je wurin kamar yadda kai ma idan ka ji ƙarar wayarta hankalinka zai koma.”
BBC Hausa (https://www.bbc.com/hausa/articles/c93lr4vpz03o?at_campaign=ws_whatsapp)




