Sojojin Isra’ila sun ce Iran ta harbo makamai masu linzami aƙalla 100

Mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila IDF, Avichay Adraee ya ce Iran ta harba aƙalla makamai masu linzami 100 a karo na biyu zuwa Isra’ila.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce an kakkaɓo akasarin makaman, yayin da wasu kuma ba su kai inda aka so su kai ba.
Hukumomi a fannin kiwon lafiya na Isra’ila sun ce mutane 40 ne harin ya shafa wanda a yanzu suke karɓar kulawa a asibitoci daban daban, kuma biyu daga ciki na cikin mawuyacin hali.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wasu jami’an Amurka biyu sun ce sojojin Amurka sun taimaka wajen kakkaɓo wasu makamai masu linzami na Iran da ta harba Isra’ila.
Tun da farko Shugaban ƙasar Donald Trump ya umarci ƙasar Iran da ta koma kan teburin yarjejeniyar makamin nukiliya da take yi da Amurka.
Trump ya kuma bayyana harin da Isra’ila ta kai wa Iran a matsayin kyakkyawa, har ma ya yi gargaɗi da cewa Isra’ilar na shirin karin wasu munanan hare-haren ma.
Ya bukaci Iran da ta hanzarta cimma matsaya a kan shirinta na nukiliya domin dakatar da ci gaban rikicin.
BBC Hausa (https://www.bbc.com/hausa/live/cwy684d517qt?at_campaign=ws_whatsapp)




