Hausawan Rivers Sun Yi Zargin Mutuwar Mambobi Hudu a Rikicin Kasuwar Oil Mill

Kungiyar Hausawa mazauna Jihar Rivers ta bayyana cewa mambobinta hudu sun rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar da ta barke a karshen makon da ya gabata a Oil Mill Market da ke yankin Rumuokwurusi a Port Harcourt.
Shugaban kungiyar, Alhaji Musa Saidu, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ya jagoranci wasu shugabannin al’ummar Arewa domin duba irin barnar da aka yi a kasuwar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
A cewarsa, baya ga asarar rayukan mambobin kungiyar guda hudu, an kuma yi wawashe tare da lalata shaguna da dama mallakin ‘yan kasuwar Arewa a yayin tashin hankalin.
Shugaban ya nuna damuwa kan yadda lamarin ya faru, yana mai kira ga hukumomi da su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma bukaci a zauna lafiya tare da karfafa zaman tare a tsakanin al’ummomin da ke zaune a jihar domin kauce wa sake aukuwar irin wannan rikici a nan gaba.




