Fursunoni, wata Mai juna biyu Suna cikin mutum 27 da aka kashe a harin da Rasha ta kai a Ukraine

Aƙalla mutane 27, ciki har da fursunoni 16 da wata mace mai juna biyu, sun mutu a hare-haren sama na Rasha a kan mafi yawan kudu maso gabashin Ukraine, a cewar Shugaba Volodymyr Zelenskyy da jami’an yankin.
Hare-haren sun zo ne da daddare a ranar Talata, kwana guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya wa Rasha sabon wa’adin “kwanaki 10 ko 12” don cimma yarjejeniyar zaman lafiya a yakin da take yi da Ukraine ko kuma ta fuskanci sabbin takunkumi mai tsauri, wanda ya rage wa’adin kwanaki 50 da ya sanya a farkon wannan watan.
Ivan Fedorov, shugaban hukumar soji a Zaporizhia, a ranar Talata ya ce Rasha ta kai hare-haren sama guda takwas a daren da ya gabata a yankinsa kadai, inda ta kai hari kan wani kurkuku kusa da birnin Zaporizhzhia.
Zelenskyy ya ce wata mata mai juna biyu na cikin mutane uku da suka mutu a wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai kan birnin Kamianske da ke tsakiyar yankin Dnipropetrovsk, inda aka nufi wani asibiti.




