Labarai
Wasu mutane biyu sun rasu a cikin masai a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata ƙaramar waya da ta faɗa a cikinta a yankin Ƙaramar Hukumar Albasu ta Jihar Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne a ranar Asabar a unguwar Bazabe da ke ƙaramar hukumar.
Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya sanar cewa ofishin kwana-kwana ya samu kiran gaggawa game da lamarin.
Ya bayyana cewa wani ɗan shekara 40 ya shiga masai domin ciro wayarsa da ta faɗa a ciki, amma sai ya maƙale a ciki.
A sakamakon haka wani mai suna Ibrahim ya shiga domin ciro shi, amma bayan ya yi nasarar sanya masa igiya, sai shi ma ya yanke jiki ya fadi a ciki.
Daga baya hukumar ta yi nasarar fito da su ta kai asibiti inda aka tabbatar cewa sun rasu.
Hukumar ta mika gawarwakinsu ga Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Ƙaramar Hukumar Albasu domin ci gaba bincike da sauran abubuwan da suka dace.




