Ketare

Shugaban Uganda Museveni ya tabbatar da aniyar tsawaita mulkinsa na kusan shekaru 40

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa, wanda zai iya kara tsawaita mulkinsa na kusan shekaru 40.

Dan shekaru 80 a duniya ya sanar da yammacin jiya Asabar cewa ya bayyana sha’awarsa ta “takarar… mukamin mai rike da tutar shugaban kasa” a jam’iyyarsa ta National Resistance Movement (NRM).

Museveni ya karɓi mulki a shekarar 1986 bayan yaƙin basasa na tsawon shekaru biyar kuma ya yi mulki tun daga lokacin.

NRM ta sauya kundin tsarin mulki sau biyu don cire iyakokin wa’adi da shekaru, ta yadda Museveni zai iya tsawaita wa’adinsa.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun zarge shi da amfani da jami’an tsaro da kuma tallafin gwamnati don murkushe masu adawa da kuma karfafa mulkinsa – zarge-zargen da ya musanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button