Labarai
Wata matar aure ta daki diyarta mai shekara 11 akan zargin daukar mata kudi naira Dari wanda yayi sanadiyar mutuwarta.

Shaidu sun bayyana cewa Khadija ta zargi Fadila da satar kuɗin, kuma cikin fushi, ta dauki wani abu ta fara dukan yarinyar, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarta.
Wasu mazauna yankin da lamarin ya auku sun ce ba wannan ne karo na farko da Khadija ke dukan Fadila ba, musamman kan abin da ya shafi kudi.
Shaidun sun ce dama suna zargin matar tana yawan gallazawa ‘yar ta ta musamman game da batutuwan da suka shafi tallan kayan da yarinyar ke yi mata a bakin titi.
Mahaifin yarinyar, Malam Mustapha Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce abin ya faru lokacin yana wurin aiki.
Sannan mahaifin ya ce tuni ya dauki gawarta zuwa garinsu da ke jihar Kano domin yi mata jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.



