Labarai
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da zargin cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin mayar da Nijeriya kan tsarin ƙasa da ke kan tafarkin jam’iyya ɗaya a ƙarƙashin mulkinsa.
Shugaban ya kore wannan zargin ne a yayin jawabin da ya yi na zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya a zauren majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja, a ranar Alhamis.
Tinubu ya ce masu tunanin cewa APC na son mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya, to tunanin nasu kuskure ne, kuma suna yin sa cikin ruɗani ne.
Sai dai shugaban ya ce wannan ba zai hana jam’iyyar APC yin maraba da duk wanda ke son shiga cikinta ba.
Sai dai Tinubun ya ce suna farin ciki da rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyun adawa kuma ba zai Basu shawarar yadda za su warware matsalolinsu ba.




