Labarai
Alhazan Sokoto Sun Karɓi Kyautar Sallah Naira 450,000 Kowane Daya

Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sokoto ya bai wa kowanne daga cikin ’yan Hajji 3,200 daga jihar Riyal 1,000 na Saudiyya, wanda yayi daidai da Naira 450,000 a matsayin kyautar Sallah.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin da ya ziyarci ’yan hajjin jihar Sokoto a Minna, inda ya taya su murnar kammala aikin Hajji cikin nasara.
Gwamna Aliyu ya ce wannan tallafin kudi na Sallah yana da nufin taimaka wa ’yan hajjin wajen shirin komawarsu gida Najeriya.
Ya bayyana gamsuwa da yadda ’yan hajjin jihar suka gudanar da ai kinsu, inda ya ce babu wanda aka samu da laifi ko karya dokokin kasar Saudiyya a lokacin da suka kwana a ƙasa mai tsarki.



