Labarai

Kungiyoyin masu bukata ta musamman sun yi kira ga hukumar zaɓe akan alqawarin da aka daɗe ana yi musu.

Kungiyoyi da sauran masu faɗa a ji na masu bukata ta musamman a Najeriya, na ci gaba da yin tuni ga hukumar zaben kasar, kan a yi ƙoƙarin cika alƙawarin da dade dayi musu, na samar da dukkan abubuwan da suka kamata domin su ma su riƙa yin zaɓe kamar sauran ‘kasar.

Daya daga cikin masu bukata ta musamman Ukashatu Lawal Diza, wanda ke da lalurar gani, ya shaida wa BBC cewa a zaben da ya gabata na 2023 hukumar ta bullo da wasu sabbin tsare tsare, wanda ta ce za a samar da tsari da zai bai wa masu bukata ta musamman damar yin zaben cikin sirri da sauki.

Amma da zaben ya zo, yace hukumar ta gaza cika musu alkawuran da ta dauka.

Ya kara da cewa , idan har ta samar da wadannan tsare-tsare ga masu bukata ta musamman, yace la shakka ta sauke hakkin dayake kanta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanad.

Daga bisani yace suna fatan Zaben 2027 hukumar INEC za ta tanadi wadannan abubuwa ga masu bukata ta musamman don su ma su yi zabe cikin kwanciyar hankali.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button