KetareLabarai

Hukumar aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ce babu asarar Rai ko guda daya a gobarar da ta tashi a wani masaukin Alhazan Najeriya dake Makkah a jiya Asabar.

Hukumar ta bayyana haka bayyana hakan cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakiyar Daraktan yada labaru ta hukumar Fatima sanda Usara,da ta fitar .

A cewar Sanarwar gobarar ta tashi ne da misalin karfe 12 na rana a wani masauki mai suna Imaratus Sanan yayin da mahajjatan Najeriya ke ci gaba da gudanar da ibadunsu a Mina.

Masaukin Alhazan na ɗauke da mahajjatan Najeriya 484

To sai dai babu wanda ya rasa ransa , kuma dukkan mahajjatan na cikin koshin lafiya a Mina Kamar yadda Sanarwar ta bayyana

Jim kadan da faruwar lamarin, Shugaban Hukumar Farfesa Abdullahi Saleh, ya kai ziyarar gani da Ido a wani yunkuri na tantance halin da ake ciki da kuma tabbatar da cewa an bai wa mahajjatan kulawar da ta dace.

Farfesa Saleh ya bayar da umarnin gaggauta kwashe mahajjatan da abin ya shafa zuwa wani sabon masaukin na daban

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button