Labarai

Jami’an tsaron Najeriya sun kashe ƴan ta’adda da dama a Neja

Jami’an hukumar tsaro ta DSS da na rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga akalla 45, a wani aikin haɗin gwiwa da suka gadanar a kusa da garin Kuchi da ke ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja da ke tarayyar Najeriya

An dai sami nasarar ce sakamakon wani harin da dakarun tsaron na Najeriya suka kai cikin sirri, a ci gaba da yaƙin da suke yi da ƴan bindiga.

Wasu majiyoyin tsaro sun bayyana cewa jami’an DSS sun bi sahun wasu ƴan bindiga ne, inda suka daƙile yunkurinsu na kai munanan hare-hare, wanda kasurgumin ɗan bindigar nan Dogo Gide da yaransa suka shirya kaiwa wasu ƙauyuka.

Majiyar ta ce bayanan sirrin da hukumar ta tattara sun nuna yadda ƴan bindigar waɗanda suka yi sansani a dajin Bilbis da ke ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, da ma wasu sassan jihar Kaduna, inda Dogo Giden ya gayyace su domin kai hari a yankin na Kuchi.

A cewar majiyar, da sanyin safiyar Litinin ɗin da ta gaba, ƴan bindiga kusan su 100 daga ƙauyukan Kaduna da Zamfara da ke ɗauke da muggan makamai suka tunkari garin Kuchi na ƙaramar hukumar Munya a jihar Neja.

Harin dai ya biyo bayan wani kisa da aka yi wa ƴan bindiga 50, wanda ya yi wa gungun na Dogo Gide mummunar barna, lamarin da ya sanya shi yin yunƙurin ɗaukar fansa a garin na Kuchi, sai dai ƴan bindiga 50 daga cikinsu sun gamu da ajalisu a ɗauku ba daɗin da suka yi da jami’an tsaron.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button