Kotu ta hana INEC amincewa da tarukan zaɓen shugabannin ADC da bangaren David Mark ya jagoranta

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) amincewa ko shiga duk wani taron jam’iyyar ADC da wani shugabanci rikon kwarya ke kokarin gudanarwa.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a hukuncin da Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yanke, kotun ta kuma haramta wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da wasu jiga-jigan jam’iyyar tsoma baki cikin ayyukan shugabannin jihohi da aka zaba.
Shari’ar ta samo asali ne daga karar da Norman Obinna da wasu shida suka shigar a madadin shugabannin jihohin jam’iyyar, inda suka kalubalanci halaccin kwamitin rikon kwarya da kuma yunkurinsa na shirya tarukan jihohi.
Kotun ta bayyana cewa irin wannan mataki ya sabawa kundin tsarin jam’iyyar da kundin tsarin mulkin kasa, inda ta jaddada cewa shugabannin da aka zaba ne kawai ke da ikon gudanar da taruka.
Mai shari’ar ta kuma ce duk da cewa kotuna ba sa yawan tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyu, amma za su shiga idan aka samu karya doka ko kundin tsari.
Saboda haka, kotun ta soke duk wani kwamitin da aka kafa don shirya tarukan, tare da tabbatar da cewa shugabannin jihohi na ADC za su ci gaba da rike mukamansu har zuwa karshen wa’adinsu ba tare da tsangwama ba.



