Ketare

Tsananin zafi: Muhimman shawarwarin da hukumomin Saudiyya suka ba maniyyata

Maniyyata sun fara gudanar da ayyukan ibada na aikin hajjin shekara ta 2025 a birnin Makkah da ke Saudiyya.

Hajji, aiki ne da ke buƙatar zirga-zirga da ayyukan motsa jiki da dama, wani abu da ya sanya hukumomi ke fadakarwa game da yanayin tsananin zafi da ake fuskanta a ƙasar daidai lokacin da ake gudanar da waɗannan ayyuka.

Hukumar lura da aikin hajji ta Saudiyya ta ce yanayin zafi zai kai maki 45 a kwanakin da ake tsaka da aikin na hajji.

Ma’ikatar, a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na sada zumunta ta ce wannan yanayi na tsananin zafi na da haɗarin jefa maniyyata cikin yanayi na galabaita da jefa rayukansu cikin hadari.

Maniyyata kusan miliyan biyu daga fadin duniya ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin, wanda ya ƙunshi ɗawafi da zaman Mina da sa’ayi da tsayuwar Arfa da kuma jifar shaiɗan.

BBC (https://www.bbc.com/hausa/articles/c0k3rzp4g4xo?at_campaign=ws_whatsapp)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button