Jakadan Shugaba Trump na musamman, Steve Witkoff ya kai ziyara domin duba wuraren da ake rabon tallafi a Gaza masu samun goyon bayan Isra’ila da Amurka da ke shan suka.

Mista Witkoff na tare da jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckerbee, wanda ya wallafa hotunan wuraren rabon tallafin.
Ziyarar tasu na zuwa ne a daidai lokacin da ake jefa wa mazauna Gaza agaji ta sama irinsa mafi girma.
Ƙasashen Jamus da Sifaniya da Belgium da Faransa da kuma Bahrain ne ke jefa tallafin tare da haɗin gwiwar ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Jordan.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan Falasɗinawa 1,400 aka kashe a ƙoƙarinsu na karɓar tallafi a Gaza tun ƙarshen watan Mayu, inda mafi yawansu aka harbe su a kusa da wuraren rabon tallafin.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch ta bayyana kashe-kashen da laifukan yaƙi.
Isra’ila na zargin Hamas haifar da yamutsi a kusa da wuraren rabon tallafin, inda ta ce ba da gayya jami’anta ke buɗe wuta kan fararen hula ba.




