Labarai

Hukumar Kare Hakkin Masu Sayayya ta Tarayya (FCCPC) ta sammaci kamfanin jiragen sama na ‘Air Peace Limited’ biyo bayan korafe-korafen kwastomominsu dangane da gazawar da kamfanin ya yi na dawo da kudaden Tikitin Jirgin da aka soke tafiyarsa.

An mika sammacin ne ta wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan hulda da kamfanoni na FCCPC, Ondaje Ijagwu, a ranar Litinin.

A cewar Hukumar, ayyukan Air Peace na iya zama ya saba wa Sashe na 130 (1) (a) da (b) da 130 (2) (b) na Dokar Kariya ta Tarayya da Kariya ta (FCCPA) 2018, wanda ke ba wa kwastomomi hakkin mayar musu da kudadensu akan lokaci idan an samu tangardar tafiya.

A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Yuni 2025, FCCPC ta yi amfani da sashe na 32 da na 33 na FCCPA, inda ta bukaci kamfanin da ya gurfana a gaban hukumar a hedikwatar ta Abuja a ranar Litinin 23 ga watan Yuni 2025.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button