Labarai

Kudin makarantar Northwest a jihar Kano ya yi tashin gwauron zabi

A kwai yiwuwar wasu daga cikin Daliban da ke karatu a Jami’ar nan mallakin jihar Kano wato Northwest za su yi Adabo da makarantar

Daliban dai sun wa yi gari da karbar umarni da ga hukumar makaranta na Karin kudin makaranta Inda a da can daliban su ke Biyan naira Dubu Talatin (30,000) kafin zuwan Gwamnatin jamiyyar NNPP

Inda a yanzu Kuma hukumar makarantar ta Umarci kowannne dalibi da ya biya naira Dubu Hamsin da Bakwai, wa’yansu Kuma Dubu Hamsin da uku a matsayin kudin makaranta.

Wani dalibi da ya ke yin karatu a makarantar Wanda ya ne mi da a sakaya sunansa ya shaida wa Jaridar Ahrasjo News ce wa wanna Kari da aka yi zai kawo barazanar rashin ci gaba da karatun mutane da yawa daga cikin Daliban jami’ar Wanda ya ce Duba da La’akari da halin kunci da ake ciki.

Wannan dai na Zuwa ne A daidai Gabar da Gwamnatin jihar Kano ke bayyana cewa tana bayar da fi_fiko a fannin Ilimi domin saukakawa ‘Yan jihar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button