Ketare

Akalla ‘Yan Jarida 128 Suka Mutu a Duniya a 2025 — IFJ

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Duniya (IFJ) ta ce akalla ‘yan jarida 128 ne suka rasa rayukansu a faɗin duniya a shekarar 2025, inda sama da rabin mutuwar suka faru ne a yankin Gabas ta Tsakiya

 

 

Rahoton IFJ ya nuna cewa lamarin ya fi muni a yankunan Falasdinu, inda aka kashe ‘yan jarida 56 sakamakon yaƙin da ke gudana tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza. Shugaban IFJ, Anthony Bellanger, ya ce adadin mutuwar ya kasance abin firgici tare da yin Allah wadai da rashin hukunta masu kai hari kan ‘yan jarida.

 

Har ila yau, IFJ ta bayyana cewa ‘yan jarida 533 ne ke tsare a gidajen yari a duniya, inda ƙasar China ke kan gaba da daure ‘yan jarida 143, ciki har da na Hong Kong. Rahoton ya kuma nuna bambancin alkaluman IFJ da na wasu ƙungiyoyi kamar RSF da UNESCO kan adadin ‘yan jaridar da aka kashe a 2025.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button