Kisan Mata da ‘Ya’yanta a Kano: Masanin Tsaro Ya Fito da Dabarun Kare Kai Guda 7

Daga Buhari Ali Abdullahi, Wakilinmu a Kano
Al’ummar jihar Kano na ci gaba da zama cikin fargaba da alhini, biyo bayan wani mummunan kisan gilla da wasu miyagu suka yi wa wata mata tare da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Charanci da ke birnin Kano.
Wannan ba shi ne karon farko da aka samu irin wannan aika-aika ba, domin kuwa ƙasa da watanni da suka gabata, an kai irin wannan hari a unguwar Tudun Yola, inda aka kashe mata biyu tare da ƙona gawarwakinsu. Waɗannan hare-hare sun jefa tsoro a zukatan mazauna jihar, waɗanda da dama ke ganin rayuwarsu na fuskantar barazana.
A wata tattaunawa ta musamman da BBC HAUSA wani mai sharhi kan harkokin tsaro a kasarnan Amb. Capt. Abdullahi Bakoji Adamu (mai ritaya), ya bayyana wasu muhimman matakai guda bakwai da ya kamata magidanta su ɗauka domin kare iyalansu daga irin waɗannan hare-hare.
A cewar masanin, “Tsaro ba aikin gwamnati ko na jami’an tsaro kaɗai ba ne; alhaki ne da ya rataya a wuyan kowa, musamman magidanta.”
Ga dabarun da ya shawarci a bi:
1. **Kulle Gida da Kula da Ƙofa:** Ya jaddada cewa wajibi ne a tabbatar ƙofofin gida a rufe suke a kowane lokaci. Kada a buɗe ƙofa ga baƙo sai an tantance ko wanene shi, kuma a hana yara buɗe ƙofa.
2. **Tsarin Fita da Shiga:** Magidanci ya sanar da iyalinsa inda zai je da kuma lokacin da yake sa ran dawowa. Idan za a aiko wani, a sanar da su sunan wanda aka aiko da kuma saƙon da yake tafe da shi don gudun maƙaryata.
3. **Inganta Sadarwa:** A riƙa kiran gida akai-akai don jin halin da iyalai suke ciki. Sannan a tabbatar akwai katin waya a koda yaushe don kiran gaggawa.
4. **Tanadin Lambobin Gaggawa:** Kowane gida ya mallaki lambobin wayar maƙwabta na gari, ‘yan banga, ‘yan sanda, da mai unguwa. A rubuta a manne a bango don kowa ya gani.
5. **Tsare Sirrin Gida:** A daina bayyana sirrin gida a waje, kamar lokacin da maigida baya nan. Haka kuma a kiyayi yadda yara ke saurin sabo da baƙi.
6. **Haɗin Kai da Maƙwabta:** A gina kyakkyawar alaƙa da maƙwabta tare da kafa tsarin tsaron unguwa. Haɗin kan unguwa na da matuƙar wahala ga masu laifi.
7. **Sanya Fitilu da Kyamarori:** Sanya fitilu a waje da cikin gida na taimakawa wajen tsorata ɓarayi. Idan akwai hali, a sanya kyamarar tsaro (CCTV).
A ƙarshe, Capt. Bakoji ya tunatar da cewa baya ga waɗannan matakan, yana da matuƙar muhimmanci a riƙa addu’o’in kariya kamar yadda addini ya koyar, domin neman tsari daga Ubangiji.




