Labarai
Tinubu Ya Yi Allah-Wadai da Kisan Matar Aure da Ƴaƴanta Shida a Kano

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kakkausar suka kan kisan gilla da aka yi wa wata matar aure, Fatima Abubakar, da ƴaƴanta shida a unguwar Chiranci da ke Jihar Kano, yana mai bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin tausayi
A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya nuna matuƙar alhini kan abin da ya faru tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da al’ummar Kano gaba ɗaya.
Ya kuma yaba wa rundunar ƴansandan Najeriya bisa gaggawar matakin da ta ɗauka wanda ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi.
Shugaban ƙasar ya umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da gurfanar da duk masu hannu a cikin kisan a gaban kotu.



