Labarai

**Rundunar ‘Yan Sandan Bauchi Ta Damƙe Wasu ‘Yan Fashi da Makami a Giade**

**Bauchi, Najeriya** – Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta sanar da samun gagarumar nasarar cafke wasu mutane shida da ake zargi da kafa ƙungiyar fashi da makami da ta daɗe tana addabar al’ummar ƙaramar hukumar Giade a jihar.

 

An samu nasarar ne biyo bayan samun ingantattun bayanan sirri da suka kai ga kwato babura da dama da wasu kayayyakin sata da darajarsu ta haura naira miliyan ɗaya.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an fara gudanar da bincike ne bayan wasu miyagu sun kai hari kan wasu mutane biyu, Mohammed Musa da Auwal Maidawa.

 

 

A cewarsa, maharan, waɗanda ke ɗauke da adduna, wukake, sanduna, da bindigar gargajiya, sun yi wa mutanen dukan tsiya kafin su yi awon gaba da kayayyakinsu.

 

Bayan samun rahoton, Baturen ‘yan sanda na yankin Giade, CSP Bello Yusuf Kumo, ya jagoranci wani samame na musamman wanda ya yi sanadiyyar kama wani matashi mai suna Aminu Abdulkadir, mai shekaru 22. Bayan an matsa masa da tambayoyi, Abdulkadir ya toni asirin sauran abokan aikinsa, waɗanda suka haɗa da Habu Musa, Adamu Samaila, da Yusuf Sabo, waɗanda dukkansu mazauna garin Giade ne.

 

Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen fasa gidaje da shaguna a cikin garin Giade da kewaye, inda suke kwashe wayoyin hannu, kayan sawa, da sauran na’urori masu daraja.

 

 

An ƙiyasta jimillar darajar kayayyakin da aka sace a kan naira miliyan 1.2.

 

Daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannunsu har da babura guda biyu, wukake masu kaifi, kayan fasa gidaje, da katinan cire kuɗi na ATM.

 

Rundunar ta ce tana ci gaba da zurfafa bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu a wannan laifi, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kuliya domin fuskantar shari’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button