Labarai

Gwamnatin Kebbi Za Ta Yi Amfani da Bikin Argungu na 2026 Wajen Jan Hankalin Masu Zuba Jari na Ƙasashen Waje

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa tana shirin yin amfani da bikin kamun kifi da al’adu na Argungu na shekarar 2026 a matsayin wata babbar dama ta jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje, da nufin bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

Hukumar Bunkasa Zuba Jari ta Jihar Kebbi (KIPA) ta tabbatar da cewa tuni wasu masu zuba jari daga nahiyoyin Turai da Asiya suka nuna sha’awarsu ta halartar bikin.

 

Hukumar ta bayyana wannan ci gaban a matsayin wata alama mai ƙarfi da ke nuna yadda bikin al’adun ke ƙara samun karɓuwa a idon duniya a ‘yan shekarun nan.

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata, Babban Daraktan Hukumar KIPA, Dakta Muhammad Kabir Kamba, ya ce gwamnatin jihar za ta yi amfani da wannan dama wajen nunawa duniya irin dimbin arzikin da jihar ke da shi a fannonin noma, ma’adanai, da kiwo.

A cewar Dakta Kamba, wannan gagarumar sha’awa da masu zuba jarin na ƙasashen waje ke nunawa, wani sakamako ne kai tsaye na irin salon mulkin Gwamna Nasir Idris, wanda ya maida hankali wajen ƙulla alaƙa da zata kawo ci gaban tattalin arziƙi da kuma sauye-sauyen da yake yi don inganta yanayin kasuwanci a faɗin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button