Dakarun Operation FANSAN YAMMA Sun Dakile Wani Harin Kwantan Bauna a Zamfara

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA (OPFY) da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma, sun nuna gagarumar jarumta da ƙwarewa bayan sun yi nasarar daƙile wani harin kwantan ɓauna da ‘yan ta’adda suka kai musu a kan hanyar Bingi zuwa Kekun Waje zuwa Gusau a Jihar Zamfara.
Harin kwantan ɓaunar, wanda ya faru a ranar 19 ga watan Janairun 2026, ya biyo bayan wasu jerin hare-hare ne masu nasara da dakarun suka kaddamar tun daga ranar 17 zuwa 19 ga watan Janairu.
A waɗancan hare-haren, dakarun rundunar ta OPFY, tare da haɗin gwiwar wasu sassan jami’an tsaro, sun gudanar da samame da kai hare-haren ba-zata a yankunan Birnin Magaji da Anka na jihar Zamfara.
A yayin waɗannan ayyukan, an yi nasarar kashe ‘yan ta’adda huɗu, yayin da wasu da dama suka tsere cikin daji da raunukan harbi. An kuma kama wasu mutane uku da ake zargi, waɗanda aka bayyana sunayensu da Isiya Kwakwatawa, Ibrahim Dan Musulu, da Makau Lamba Goma.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan sun haɗa da:
* Babbar bindiga kirar PKT guda ɗaya
* Bindigogin AK-47 guda biyar
* Mujallun bindigar AK-47 guda uku
* Tarun harsasai na musamman (7.62mm)
* Rediyon sadarwa na Baofeng
* Babura guda uku
Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke ƙara zafafa kai hare-hare a maɓoyar ‘yan ta’adda a faɗin jihar.
N T A




