Labarai

Tsohon Hafsan Sojojin Najeriya ya zargi wasu ‘yan siyasa da hannu a matsalar tsaro

Tsohon Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Lucky Irabor mai ritaya, ya bayyana cewa matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita ta samu nasaba da rawar da wasu ‘yan siyasa ke takawa a bainar jama’a da kuma bayan fage.

 

Janar Irabor, wanda ya yi wannan bayani a wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, ya yi zargin cewa akwai wasu masu fada a ji a gwamnati da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci, tare da amfani da su don cimma manufar siyasa.

 

Ya ce, duk da cewa wadannan mutanen na nunawa jama’a tamkar suna bayar da gudummuwa wajen yaki da matsalar tsaro, hakikanin gaskiya ita ce suna da hannu wajen kada wa kasar gaba ta hanyar haddasa tashe-tashen hankali da kisa, da kuma satar jama’a a sassa daban-daban na Najeriya.

A cewarsa, galibin hare-haren da ake yi a fadin kasar na da alaka da yadda wasu ‘yan siyasa ke tallafawa kungiyoyin da ke aiwatar da su, domin neman tasiri ko cimma manufar siyasa.

 

Wannan furuci na tsohon hafsan ya kara tayar da tambayoyi daga bangaren ‘yan Najeriya, wadanda ke neman sanin ko akwai wani mataki da hukumomi za su dauka don gano mutanen da ake zargin da kuma gurfanar da su a gaban shari’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button