NDIC zata dauki tsauraran matakai na tabbatar da tsaron kuɗin jama’a

Daraktan gudanarwa na Hukumar Inshorar Ajiya ta Najeriya (NDIC), Mr. Thompson Oludare Sunday, ya bayyana cewa hukumar ta kara tashi haikan don kare kudin jama’a, tare da fadada inshorar ajiya domin tabbatar da kwanciyar hankali a tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasar.
Ya bayyana hakan ne a yayin rana ta musamman ta NDIC a bikin Kano International Trade Fair karo na 46, da kungiyar KACCIMA ta shirya, wadda aka gudanar karkashin taken: “Empowering SMEs for Sustainable Development.”
A jawabinsa, Sunday ya yaba wa KACCIMA bisa shirya baje kolin da ya ci gaba da taka rawar gani wajen bunkasa kirkire-kirkire, hada jama’a da ‘yan kasuwa da karfafa ilimin harkar kudi.
Ya ce tun tsawon shekaru 37, NDIC na taka muhimmiyar rawa wajen kare kuɗin masu ajiya musamman talakawa, tare da kula da lafiyar tsarin bankuna,
A cewar Sunday, hukumar ta kara yawan inshorar ajiya zuwa:
N5,000,000 ga masu ajiya a bankunan kasuwanci, mobile money operators, da bankunan ba da riba
N2,000,000 ga bankunan microfinance, primary mortgage, da payment service banks
Ya ce wannan karin ya bai wa NDIC damar kare kashi 99% na masu ajiya a Najeriya.
Ya bayyana cewa a duk lokacin da banki ya gaza, masu ajiya za su fara karɓar kudin inshora kai tsaye, sannan sauran kuɗi su zo daga raba kadarorin bankin a bisa kima, domin tabbatar da adalci.
NDIC ta kuma shawarci jama’a da su daidaita BVN da sunan da ke takardu na hukuma, domin samun kudinsu cikin sauri idan an samu matsala.
Ya tabbatar da cewa duk da wa’adin Maris 2026 da aka bai wa bankuna su kara jari, NDIC da CBN sun shirya tsaf don tabbatar da yanayi mai dorewa, ba tare da barazana ga masu ajiya ba.
Sannan Ya yi kira ga mahalarta baje kolin da su ziyarci rumfar NDIC domin samun karin bayanai kan inshorar ajiya, tsare-tsaren banki, da kariyar dukiyoyinsu.
A karshe, Sunday ya gode wa KACCIMA, sarakuna, bak’i da ‘yan jarida, tare da yi wa mahalarta fatan samun baje koli mai albarka.



