Labarai

Kungiyar One Kano Agenda ta yaba wa Gwamnatin Kano kan kokarinta na magance matsalar tsaro

Kungiyar One Kano Agenda ta jinjinawa Gwamnatin Jihar Kano bisa matakan da ta ke dauka don dakile barazanar tsaro da ta fara kunno kai a wasu sassan jihar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai da ta gudanar a dakin taro na cibiyar ‘yan jarida ta jihar Kano, inda ta ce jajircewar gwamnati a wannan lokaci ya nuna mahimmancin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Haka zalika kungiyar tayi kira ga jama’ar Kano da su ci gaba da tallafawa jami’an tsaro da bayanai masu amfani, don tabbatar da cewa duk wani matsugunin ta’addanci ya gaza samun tushe a jihar.

A cewar kungiyar, One Kano Agenda aikin ta ne ganin zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali sun tabbata, tare da samar da yanayi da zai ba dukkan al’umma damar gudanar da harkokinsu cikin lumana.

Kungiyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga dokar hana achaba a wasu yankuna da gwamnati ta haramta, tana mai cewa matakin ya dace da yanayin tsaro da ake ciki kuma zai rage hada-hadar miyagun ayyuka.

Hakazalika, One Kano Agenda ta yi Allah wadai da kiraye-kirayen da wasu ke yi na a saka dokar ta-baci a Kano, tana mai cewa hakan ba zai taimaka ba, illa dai zai haddasa tashin hankali da tabarbarewar harkokin yau da kullum.

Kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da mara wa gwamnati baya tare da yin aiki tukuru domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a fadin jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button