Gwamna Abba zai samar da jiragen leken asiri don tsaurara tsaro a kan iyakar Kano da Katsina

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatin jihar na samar da jiragen leken asiri (drones) da wasu kayan aiki na musamman domin kara sa ido da gaggauta daukar mataki kan barazanar tsaro a yankunan da ke kan iyakar Kano da Katsina.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Laraba, bayan ziyarar gwamnan ga sansanonin dakarun hadin gwiwa (JTF) a Tsanyawa da Shanono, inda suka fuskanci hare-haren ‘yan bindiga a kwanakin baya.
Gwamna Abba ya roki al’ummar yankunan da abin ya shafa da su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro da bayanai masu amfani game da motsin ‘yan bindiga, domin kawo karshen ta’addancin da ya addabi yankin.
Ya bayyana cewa yayin da ya ziyarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan lamarin, shugaban kasan ya nuna goyon bayan gaggawa ga bukatun da aka gabatar masa domin magance matsalar.
Gwamnan ya umurci dakarun JTF da su kara kaimi wajen ganin an kubutar da mutanen da aka sace a Tsanyawa da Shanono, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen ganin sun koma ga iyalansu.
“Mun san irin barnar da ake yi a wadannan yankuna, an rasa rayuka, an kuma yi garkuwa da mutane. Ina tabbatar muku, in sha Allah, wadanda aka sace za su dawo cikin koshin lafiya,” in ji shi.
Gwamna Abba ya bayyana damuwarsa kan yadda irin wannan matsalar tsaro ta fara bayyana a Kano, inda ya ce lamarin sabo ne ga jihar, amma ana daukar matakai tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin shawo kan abin.
Ya kuma tabbatar wa jami’an tsaro cewa gwamnatin sa za ta dauki duk matakan da suka dace don inganta jin dadinsu da kuma ba su kayan aiki na zamani.
A yayin rangadin, gwamnan ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su, tare da basu tabbacin cewa gwamnati tana aiki tukuru domin ganin an sako su.
Rahotanni sun nuna cewa akalla mutum biyar aka sace a Tsanyawa, sannan mutum goma a Shanono, inda kuma aka rasa rayuwar wata mata yayin harin.




