Labarai
Wasu Mahara Sun Kai Hari Gidan DPO a Jigawa, Sun Kashe Jami’in Dan Sanda guda 1

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da harin da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai gidan baturen ’yan sanda (DPO) na Aujara, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’i guda.
Mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya ce harin ya faru ne da safiyar ranar 25 ga Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, lokacin da maharan suka farmaki gidan DPO ɗin. Ya bayyana cewa jami’an da ke bakin aiki sun yi musayar wuta da maharan, sakamakon haka jami’i ɗaya ya rasa ransa, yayin da wani ya samu rauni.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ya mika ta’aziyya ga iyalan mamacin, tare da tabbatar da kaddamar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan aiki da tabbatar da hukunta su.




