Siyasa
Naja’atu Muhammad: “Babu Dabarar da Za ta Kawo Tinubu Nasara a 2027”

Fitacciyar ’yar gwagwarmayar siyasa, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai sake samun nasara a zaben 2027 ba, duk da irin matakan da ake zargin gwamnati ke ɗauka don tilastawa ’yan kasa shiga jam’iyyar APC.
Naja’atu ta ce ko da gwamnati tana amfani da tsoro ko matsin lamba kan jama’a, hakan ba zai sauya ra’ayin mutane ba, domin a cewarta, “jama’a sun farka.”
Maganganunta sun jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke goyon bayanta, yayin da wasu ke ganin cewa kalamanta na siyasa ne kawai.




