Labarai

Kotu ta yankewa Najiyullahi Alkasim hukuncin kisa ta hanyar rataya

Babbar kotun jihar Kano da ke Miller Road, karkashin jagorancin Mai Shari’a Farida Dan-Baffa, ta yanke wa Najiyullahi Alkasim hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same shi da laifin kashe Isyaku Yau a wani bikin wasan DJ da aka gudanar a unguwar Dawakin Dakata.

Lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soran-Dinki, ya gabatar da shaidu hudu, yayin da wanda ake tuhuma ya tabbatar da kare kansa da shaidu uku. Bayan nazarin hujjojin bangarorin biyu, kotu ta bayyana cewa an tabbatar da laifin kisan kai, wanda ya sabawa sashi na 221 na Penal Code.

Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a wajen taron, inda Alkasim ya caka wa marigayin sukundiriba a  wuya, wanda ya yi sanadin mutuwarsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button