Kano: Kungiyar Masu Bukata Ta Musamman Na Kira Ga Gwamnati Kan Kafa Hukumar Kulawa da Su

Kano, 2 Disamba, 2025 –Shugaban reshen jihar Kano na Kungiyar Kare Hakkin Masu Bukata Ta Musamman Ta Kasa, Eng. Usman Gurgu Dakata, ya yi kira ga gwamnan jihar Kano, kananan hukumomi, da ‘yan majalisa da su yi amfani da ranar 3 ga watan Disamba, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Masu Bukata Ta Musamman, wajen aiwatar da dokar kafa hukumar da za ta kula da harkokin masu bukata ta musamman a jihar.
A yayin zantawar sa da manema labarai ciki har da wakilin Ahrasjo News, Dakata ya bayyana cewa wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya sun riga sun kafa irin wannan hukuma, amma jihar Kano har yanzu ba ta aiwatar da hakan ba.
Eng. Dakata ya ce kafa wannan hukuma zai taimaka wajen inganta rayuwar masu bukata ta musamman, musamman a fannonin tsaro, lafiya, ilimi, sana’o’in dogaro da kai, da sauran muhimman al’amura.
A karshe, ya yi fatan mahukunta za su duba halin da masu bukata ta musamman ke ciki a jihar Kano domin kawo musu tallafi da kariya, tare da tabbatar da cewa suna samun hakkokinsu kamar yadda doka ta tanada.




