Jam’iyyar APC a karamar hukumar Dala Ta Tsayar da DSP Barau Jibrin Maliya a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Kano a 2027

dandazon mambobin jam’iyyar APC na karamar hukumar Dala sun gudanar da bikin tsaida DSP Barau Jibrin Maliya a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a zabukan 2027.
Taron ya gudana ne a babban dakin taro na Mumbayya House da ke Gwammaja, inda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga jihar Kano. Mahalarta taron sun bayyana gamsuwa da gudunmawar DSP Barau Jibrin Maliya ga al’ummar Kano da jam’iyyar, tare da kira ga jam’iyyar ta bashi tikitin takara kai tsaye saboda kwarewa da sanin makamar aiki da suke ganin ya nuna.
Taron ya gudana karkashin jagorancin tsohon dan majalisar jiha da tarraya, Comrade Al-Hasan Uba Idris, wanda shi ne shugaban kungiyar Tinubu-Barau Support Mobilization karkashin Hon. Sidi Kabuwaya.
A yayin taron, Comrade Idris ya raba tallafi ga mambobin jam’iyyar sama da 550, inda kowane mutum ya karbi N30,000,
Daga karshe, taron ya shaida karbar gungun mambobin jam’iyyar PDP wadanda suka fice daga jam’iyyarsu suka shiga APC, tare da bayyana aniyarsu ta mara wa Sanata Barau baya domin ya kai ga zama gwamnan Kano.
S.A Muktar B.A.A Gwammaja (MC)




