Labarai
Gwamnonin Arewa Sun Bukaci Dakatar da Hako Ma’adinai na Watanni Shida Don Magance Matsalar Tsaro

Kungiyar Gwamnonin Arewa tare da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta yankin sun ba da shawarar a dakatar da dukkan ayyukan hakar ma’adinai a Arewa na tsawon watanni shida, sakamakon ƙara tsananta matsalar tsaro a yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa dakatar da ayyukan hakar ma’adinai zai bai wa hukumomi damar nazari da tantance alakar da ke tsakanin hako ma’adinai da ayyukan ta’addanci, tare da ƙirƙirar sabbin matakai na tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.
Haka kuma, shugabannin yankin sun jaddada bukatar gwamnatin tarayya ta samar da ingantattun matakan tsaro da kayan aiki ga jami’an tsaro domin dakile barazanar da ke kara tsananta a yankin.



