Labarai
Gobara Ta Hallaka Mutum Biyar ’Yan Gida Ɗaya a Kofar Sauri, Katsina

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Litinin ta kashe mutum biyar ’yan gida ɗaya a unguwar Kofar Sauri, cikin birnin Katsina. Shaidu sun ce wutar ta kama gidan ne da dare, ta bazu cikin sauri, ta kuma ƙone gidan baki ɗaya kafin maƙwabta su samu damar kai agaji.
Mutanen da suka rasu sun haɗa da mahaifi, mahaifiya da ’ya’yansu uku, waɗanda suka makale a cikin gida lokacin da gobarar ta yi ƙamari.
Wasu mazauna yankin sun danganta lamarin da matsalar wutar lantarki da aka dawo da ita a lokacin, yayin da wasu ke ganin iska mai ƙarfi ta taimaka wajen bazuwar wuta cikin sauri.
Hukumomin ’yan sanda da na kashe gobara a jihar ba su fitar da cikakken rahoto kan musabbabin gobarar ba, ko matakan bincike da ake ɗauka a halin yanzu.




