Labarai

Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar Ya Yi Murabus

Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa daga ranar 1 ga Disamba, 2025, bisa dalilan lafiya.

A wasikar da ya aika wa Shugaba Bola Tinubu, Badaru ya bayyana cewa matsalolin lafiyarsa ne suka sa ya ajiye aiki. Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin, tare da gode masa bisa hidimar da ya yi wa ƙasa.

Ana sa ran shugaban zai sanar da majalisar dattawa sabon ministan tsaro a cikin wannan makon.

Badaru, mai shekaru 63, ya kasance gwamnan jihar Jigawa sau biyu daga 2015 zuwa 2023, kafin nadinsa a matsayin minista a ranar 21 ga Agusta, 2023.

Murabus ɗin nasa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar gaggawa kan harkokin tsaro a fadin ƙasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button