Jigawa: ’Yan Sanda Sun Kama Mutum Ɗaya, Sun Kwato Babura Biyu Bayan Harin ’Yan Fashi a Sule Tankarkar

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta cafke mutum ɗaya da ake zargi da fashi da makami, yayin da wasu biyu suka tsere, bayan da suka shiga gidan wani mutum mai suna Shamsu Muhammad a kauyen Togai, ƙaramar hukumar Sule Tankarkar, inda suka sace sabbin babura biyu (2) na Boxer.
Lamarin ya faru ne bayan mutanen uku ɗin sun kutsa gidan cikin dare dauke da makamai, inda suka yi awon gaba da baburan. Da zarar jami’an ’yan sanda suka samu kiran gaggawa, sai suka hanzarta zuwa wajen domin ceto al’amura.
Yayin da ’yan fashin ke ƙoƙarin tserewa, ɗaya daga cikinsu ya shiga asibitin yanking domin boye ɗaya daga cikin baburan da suka sace, sai dai jama’a suka gano shi suka yi masa dukan kawo wuka, kafin ’yan sanda su iso su karɓe shi daga hannunsu.
A ranar 27 ga Nuwamba, 2025, an yi nasarar kwato bindiga ɗaya ta baridu da babura biyu na Boxer, wanda aka sace, daga hannun wanda aka kama.
Rundunar ’yan sanda ta ce tana ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere, yayin da wanda yake hannun su zai gurfana a kotu bayan kammala bincike.




