Labarai

Gwamnatin Jihar pilato Za ta Hada Gwiwa da Kasar China da Manyan Kamfanoni don Bunkasa Kasuwanci da Yawon Buɗe Ido

Gwamnatin Jihar Pilato ta bayyana shirin haɗin gwiwa da wasu manyan kamfanoni da kuma Kasar China domin inganta harkokin kasuwanci, masana’antu da yawon buɗe ido a jihar, tare da amfani da arzikin da Plateau take dashi

 

Kwamishinan Ciniki da Masana’antu na Jihar Pilato Muhammad Salihu Nyalun, wanda ya wakilci jihar a baje-kolin da hukumar Ciniki da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ya bayyana cewa ziyartar ta ba su damar nuna irin albarkatun da Plateau ke da su — musamman ma’adinai, wuraren yawon buɗe ido da damar zuba jari.

 

Ya ce tattaunawar da suka yi da manyan kamfanonin duniya, ciki har da wakilai daga Kasar China, ta buɗe sabon babi na haɗin gwiwa da zai iya janyo jari mai yawa don farfado da tattalin arzikin Pilato

 

A yayin baje-kolin, jihar Kano ta karrama gwamnan Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, bisa irin rawar da yake takawa wajen kawo ci gaba da karfafa zumunci tsakanin jihohi.

Gwamnatin pilato ta ce ci gaba da tattaunawa da kamfanoni da ƙasashen waje na daya daga cikin manyan matakan da ake ɗauka domin samar da ayyukan yi, raya masana’antu, da bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button